Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito yadda a cikin majalisar dokokin ƙasar Tanzania, wakilan majalisar suka tarbi gabatarwa da kuma sanarwar gabatar da mataimakin jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da dogon tafi na ban girma.
Hotunan sun nuna daidai lokacin da mambobin majalisar suka yi wa wakilin na Iran da kyakkyawar tarba. Haka kuma, a cikin bidiyon ana iya ganin martanin jakadan haɗaddiyar daular Larabawa (UAE), wanda ya bayyana a matsayin wanda bai ji daɗi ba kuma ya shiga cikin damuwa (ko kunya) yayin da daukacin majalisar take tafi ga wakilin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ra'ayinka